A halin da ake ciki kuma kungiyoyin gwagwarmaya sun yi kira ga Falasdinawa da su halarci sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa a gobe tare da sanar da shiga yajin aikin gama gari.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Wafa cewa, ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankunan Palasdinawa da aka mamaye tun daga farkon watan Ramadan da kuma ci gaba da hare-haren da sojojin yahudawan sahyoniya suke kaiwa birnin Kudus da al'ummar Palastinu.
Kungiyar Fatah a yammacin Larabar nan ta yi Allah wadai kan shiru da kasashen duniya suke yi kan kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ke yi wa al'ummar Palastinu da kuma ci gaba da kai hare-hare a wurare masu tsarki musamman masallacin Al-Aqsa, tare da cewa: Wannan shirun na karfafawa gwamnatin mamaya kwarin gwiwar aikata laifukan da suka shafi al'ummar Palastinu.
Kungiyar ta kara da cewa: Al'ummar Palastinu za su ci gaba da kasancewa masu kare kasar Palastinu da kuma tunkarar wuce gona da iri da laifukan gwamnatin mamaya.
Dakarun mamaya sun harbe wani matashi Bafalasdine dan shekaru 14 a kauyen Hassan da ke yammacin birnin Bethlehem da yammacin jiya.
Wannan shi ne shahidi na biyu Bafalasdine daga wannan kauyen da ya yi shahada a cikin kwanaki ukun da suka gabata.
A ranar Litinin din da ta gabata, Ghada Sabatin, wata Bafalasdine 'yar kauyen, ta yi shahada.
A jiya ne dakarun mamaya suka harbe Mohammad Hassan Assaf, Bafalasdine mai shekaru 34 a kauyen Kafr al-Laqaf da ke cikin garin Qalqiliyah, a wani hari da suka kai a birnin Nablus, yayin da wasu 33 suka samu raunuka ta hanyar harsashi mai rai ko roba.