IQNA

Hukuncin Dauri a kurkuku kan wadanda suka kai hari a Masallacin Minnesota

21:59 - April 14, 2022
Lambar Labari: 3487169
An yanke wa wadanda suka kai hari a wani masallaci a jihar Minnesota ta Amurka hukuncin dauri a gidan kaso.

A cewar kafar yada labarai ta ABC News, mutanen biyu daga jihar Illinois da ke da hannu wajen kai harin bam a wani masallaci a jihar Minnesota a shekarar 2017, an yanke musu hukuncin daurin shekaru 35 a gidan yari, amma saboda hadin kai da ba da shaida kan wanda ya shirya wannan ta'addanci, bisa bukatar wadanda abin ya shafa da kuma masu gabatar da kara, An yanke musu hukuncin dauri na kasa da akalla shekaru 35 a gidan yari.

Michael McWhorter, mai shekaru 33, an yanke masa hukuncin daurin kasa da shekaru 16 a gidan yari da kuma Joe Morris mai shekaru 26, shekaru kusan 14 a gidan yari.

Dukansu sun riga sun ba da shaida a cikin shari'ar wadda aka fara a 2020 kan cewa Emily Claire Hari, shugaban wata karamar kungiyar  'yan bindiga a  Illinois da ake kira White Rabbits.

A karshen shekarar 2020 ne aka yanke wa Hari hukuncin daurin shekaru 53 a gidan yari a shekarar da ta gabata ce ta, saboda kai hari a cibiyar Musulunci ta Dar al-Farooq, da wani masallaci da ke wajen birnin Minneapolis.

A cewar jaridar Star Tribune, Alkalin kotun Donovan Frank ya ce  hadin kan da wadannan mutane suka bayar, hakan ya ba shi damar zartar da hukunci kasa da hukuncin da ya dace da su bisa doka.

A ranar 5 ga watan Agustan 2017 ne wani bam ya tashi a ofishin Limamin Masallacin Al-Farooq da Cibiyar Musulunci, Duk da cewa babu wanda ya jikkata sakamakon tashin bam din, harin ya haifar da firgici a tsakanin musulmin yankin.

A cewar limamin masallacin, harin ya rage yawan masallata a masallacin. Sai dai Imam Mohammad Omar, babban darektan cibiyar Islama ta Darul Farooq, ya yi kira ga malamai da shugabannin addini da su sanya hannu a budaddiyar wasikar neman gwamnati ta dauki matakin ba su kariyar da ta dace.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4049101

captcha