IQNA

22:09 - April 16, 2022
Lambar Labari: 3487174

An Bayar da izinin saka hijabi na wucin gadi ga daliban Laberiya

Tehran (IQNA) Gwamnatin kasar Laberiya ta ba da umarnin kafa tsarin hadaddiyar kungiyar makarantu na Musulmai da Kirista domin baiwa dalibai damar sanya hijabi na wani dan lokaci a cikin watan Ramadan.

An Bayar da izinin saka hijabi na wucin gadi ga daliban Laberiya

A cewar kungiyar sa ido ta kan hakkokin bil adama ta Laberiya, wannan shi ne karo na farko a kasar Laberiya da aka baiwa dalibai ‘yan makaranta damar sanya hijabi.

Matakin dai ya biyo bayan matsin lamba na shekaru da dama daga shugabannin addinin Islama ne da ke korafin rashin mutunta Sallar Idi a karshen watan Ramadan, idan aka kwatanta da na kiristocin.

A shekarar 2019, gwamnatin kasar ta ba wa ma’aikata Musulmi damar gudanar da bukukuwan Sallar Idi a karon farko a tarihin kasar Laberiya.

Wani mataki kuma shi ne nada Osman T. Jaloo a matsayin mashawarcin shugaban kasa musulmi na farko a kasar, da zai yi aiki tare da wasu mashawarta kiristoci biyu da kuma baiwa shugaban kasar shawara kan batutuwan da suka shafi al'ummar musulmi.

Bisa kididdigar da aka yi a kasar Laberiya a shekarar 2008, kashi 85.6 na al’ummar kasar Kirista ne, kashi 12.2 kuma Musulmi ne. Kashi 1.4 cikin 100 na da'awar cewa ba su da addini, kashi 0.6 cikin 100 na bin akidar addini na gargajiya, kuma adadin mutanen kasar Laberiya a jimlace ya kai kusan mutane miliyan uku da rabi.

 

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4049238

captcha