IQNA

Ana Ci Gaba Da Yin Allawadai Da Hare-Haren Isra'ila A Kan Masallacin Quds

22:54 - April 16, 2022
Lambar Labari: 3487175
Tehran (IQNA) ana ci gaba da yin tir da Allawadai da hare-haren Isra'ila a kan masallacin Aqsa.

Rahotanni sun bayyana cewa Masana da kungiyoyin kare hakki dan adama da dama a kasashen Musulmi sun yi tir da hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan alummar falasdinu musamman a masallacin qudus jiya jumaa kana sun bukaci Alummar duniya da su nuna goyon bayansu ga Alummar falasdinu game da zaluntarsu da isra’ila ke yi.

Dakarun kare juyin musulunci na iran IRGC a cikin wani bayani da suka fitar sun yi tir da mummunan harin da sojojin Isra’ila suka kai kan masallata a masallacin kudus mai tsarki inda suka bayyana hana a matsayin keta hurumin wurin mai tsarki na musulmi

Anata bangaren Cibiyar hadin kan musulmin Afrika ta kudu ta yi tir da harin baya bayannan a masallacin Qudus a jiyar Juma’a da yayi sanadiyar jikkata mutane 158 bayan da rikici ya barke tsakanin falasdinawa masu zanga-zanga da sojojin Isra’ila.

Rikicin ya barke ne yan sao’I bayan da sojojin Isra’ila suka kashe wani bafalasdinu a garin jenin dake gabar yammacin kogin Jodan,

captcha