A ‘yan kwanakin da suka gabata ne shugaban kasar Tunisiya Kais Saied ya sanar da rusa majalisar dokokin kasar, bayan dakatar da aikinta tun ranar 25 ga watan Yulin 2021.
A cikin wani jawabi da Qais Saeed ya yi, ya ce, "Bisa doka ta 72 a kundin tsarin mulkin kasar, a yau, a wannan lokaci mai dimbin tarihi, na sanar da rusa majalisar dokokin kasar, domin kiyaye kasa da cibiyoyi, da kuma kiyaye al'ummar kasar Tunisia."
Shugaban ya yi la’akari da cewa taron wasu ‘yan majalisar wakilai da aka dakatar da aikinsu daga nesa, wani yunkuri ne na juyin mulki da bai yi nasara ba, inda ya bayyana cewa sun shirya makarkashiyar ta’addanci a cikin gida da waje.
Ya jaddada cewa za a tuhume su da laifi, kuma Ministan Shari’a ya dauki matakin shigar wata kara a gaban masu gabatar da kara.
Shugaban ya yi gargadin cewa duk wata hanya ta tashin hankali za ta fuskanci doka, domin a cewarsa jihar ba za ta taba zama abin wasa a hannun wadanda suka yi yunkurin kifar da ita ba.
Da yake jawabi ga 'yan Tunisiya, Saeed ya ce, "Mu duka mu zauna lafiya, domin cibiyoyin gwamnati ne akwai za su kare kasar daga masu tsattsauran ra'ayi da manufarsu ta rusa kasa" a cewarsa.
Dangane da taron majalisar dokokin kasar da aka dage, wanda ya gamu da cikas, shugaban kasar Tunisiya ya bayyana a ganawarsa da firaministan kasar Najla Boden cewa, fitina ta fi kisa tsanani, inda ya kara da cewa, "Idan har ana son a raba kasar da haifar da fitina, to, a kakkae hannu masu son tayar da ita.
Qais Saeed ya jaddada cewa "abin da suke yi wata makarkashiya ce a fili ga tsaron kasa."
Ya kara da cewa, "An ba mu amanar tsaron kasar Tunisia, hadin kai da ci gaba, kuma ba za mu bari masu cin zarafi su ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati ba."
Ya kara da cewa, "Ba za mu bar su su ci gaba da ayyukansu da ke bayyana a kasashen waje ba."
To sai dai sanar da rusa majalisar dokokin kasar ta Tunisia da shuagaban kasar Qais Saeed ke da wuya, sai bangarorin siyasa suka fara yin kira da a gudanar da zaben ‘yan majalisa cikin watanni uku masu zuwa, domin kaucewa komawa zuwa ga halin da aka baro a baya na kama karya, inda shugaban kasa yake cin karensa babu babbaka.
To amma Shugaban na Tunisiya ba za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki cikin watanni uku masu zuwa ba.
Saeed ya kara da cewa, “A jiya sun yi maganar zabe nan da watanni 3 kamar yadda doka ta 89 ta tanada, ban san daga ina suka fito da wannan fatawar ba.
A baya Saeed ya ce zai kafa wani kwamitin da zai sake gyara kundin tsarin mulkin kasar , wanda za a kada kuri'ar raba gardama a kansa a watan Yuli, sannan zai gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a watan Disamba.
A gefe guda kuma, shugaban jam'iyyar Free Constitutional Party, Abeer Moussa, ya ce: "Saeed ba shi da wani zabi a karkashin kundin tsarin mulkin, kuma dole ne ya kira zabe a cikin watanni 3."
A nasa bangaren, shugaban kungiyar Ennahda, Rashed Ghannoushi, ya ce, kungiyar ta yi watsi da matakin rusa majalisar dokokin da Qais Said ya dauka, kuma za ta kaurace wa duk wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a da ke neman ta sake fasalin tsarin siyasa ba tare da izini ba.
A daya hannun kuma, kungiyar kwadago ta Tunisiya ta yi maraba da rusa majalisar dokokin kasar, tana mai cewa: "Babu bukatar majalisar ta ci gaba da aikinta da aka dakatar."
Matsayin bangarorin siyasa a Tunisiya ya banbanta dangane da matakin da shugaba Kais Saied ya dauka na rusa majalisar dokokin kasar, yayin da kungiyar Ennahda ta dauki matakin kiran abin da Qais Saeed ya yi da cewa haramtacce ne, kuma ba ta fidda ran cewa za a kai mata hari a matsayinta jam'iyya ba bayan daukar wannan mataki.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka bukaci wakilai da dama da suka halarci zaman majalisar da su gurfana a gaban rundunar yaki da ta'addanci bisa zargin hada baki da wasu bangarori da basu da halasci wajen aiwatar da abin da ya sabawa doka, bisa ikirarin gwamnatin Qais Saeed.
Mai bai wa shugaban kungiyar Ennahda shawara kan harkokin siyasa Riad Al-Shuaibi ya ce: “Mun yi watsi, kuma mun yi Allah wadai da matakin kiran wakilan da suka halarci zaman taron majalisa ta hanayar hotunan yanar gizo.
Wakilai 120 da suka halarci zaman, wadanda ke wakiltar kashi 60 cikin 100 na ‘yan majalisar. Rusa Majalisar ya zo ne bayan rusa majalisar koli ta shari’a da Qais saeed ya yi, wadanda kuma su ne manya-manyan cibiyoyi biyu a kasar a bangaren mulki baya ga bangaren gudnarwa.
Jam'iyyar Republican, daya daga cikin membobi na Coordination of Social Democratic Parties, tare da Democratic Current, da Democratic Bloc, su ce rusa majalisar wani lamari ne mai hatsarin gaske kuma, za su fuskanci lamarin ta duk wata hanya ta doka.
Babban sakataren jam'iyyar Republican Issam Shebbi ya ce: "Wannan shawarar da suka yanke ba za ta haifar da wata matsala ba, ko kara rura wutar rikici ba, ya ce aikinsu shi ne matsin lamba, kuma suna yin kira ga dukkanin bangarori na siyasa jam’iyyu da kuma masu cin gashin kansu, da su ci gaba da kara matsa lamba kan shugaban kasar ta hanyoyi nasiyasa da demokradiyya, domin ya janye wannan hukunci mai hatsarin gaske."
Jam'iyyar People's Movement, wacce ta bayyana goyon bayanta ga shugaba Kais Saied, ta bayyana abin da ya yi da cewa, zai taimaka wajen gaggauta wajen aiwatar sauye-sauyen siyasa a kasar.
Jagoran jam’iyyar ta People's Movement Moncef Bouzazi ya ce: "Abin da muke nema daga shugaban kasa yana da alaka da sauye-sauyen siyasa, dole ne a dauki lamarin a matsayin wani lamari da ya shafi dukkan al'ummar Tunisiya, kuma yana da kyau a shata sabon fasali na aiki a mataki na gaba, bayan sanar da rushe majalisar.
Yayin da al’amuran siyasa ke kara tabarbarewa, hakan zai kara taimaka ma bukatar samar da mafita ta hakika tsakanin bangarorin siyasa da al’ummar kasa.
Ga dukkanin alamu matakin na Qais babu gudu babu ja da baya a kansa, to amma abin tambaya akai shi ne wane rin shiri ne ya yi wajen fuskantar kalubalen da ke a gabansa, wajen warware matsaloli na tattalin arziki da suka addabi kasar, da kuma sauran batutuwa da suka shafi rayuwar al’ummar kasar musamman ma batun samar da ayyukan yi ga matasa, wanda kuma duk wani kure da za a iya samu wajen daukar matakai na gaba, ka iya haifar da kara rincabewar lamurran siyasa da ke fama da dambarwa a kasara halin yanzu, musamman bayan daukar matakin rusa bangarorin shari’a da majalisar dokoki, da kuma shi ga kafar wando daya da bababr jam’iyyar masu kishin Islama ta Ennahda, wadda take da dimbin magoya baya da kuma bababn tasiri a ta fuskokin siyasa da zamantakewar al’ummar Tunisia.