IQNA

Yadda aka saukar da Alkur'ani a daren lailatul kadari

16:06 - April 19, 2022
Lambar Labari: 3487189
Tehran (IQNA) Yadda aka saukar da Alkur'ani mai girma na daya daga cikin muhimman batutuwan da ake mayar da hankali a kan a cikin bahasi na ilimi, kuma wasu ayoyin kur'ani sun yi bayani kan wannan lamari.

Bayyanar wasu ayoyi na Alkur'ani ya tabbatar da saukarsa baki daya a daren lailatul kadari, wanda ya sanya wannan dare mai muhimmanci a tsakanin musulmi.

“Watan Ramadan da aka saukar da Alkur'ani a cikinsa.” (Al-Baqarah: 185) An saukar da Alkur’ani mai girma a cikin watan Ramadan mai alfarma. Kuma Allah ya ce: Ina rantsuwa da Littafi Mabayyani, Lallai ne mu mun saukar da shi a cikin wani dare mai albarka, kuma mun kasance masu gargadi. (Surat Dukhan 1/3)

A wani wurin kuma a cikin Alkur’ani muna karanta cewa: “Lalle ne, mun saukar da shi a cikin daren (Lailatul) kadari” (Qadr/1), wanda ya bayyana a sarari cewa lokacin saukar Alkur’ani a cikin dare guda shi ne daren lailatul kadari.

Daga dukkan wadannan ayoyi guda uku za a iya fahimtar cewa a cikin watan Ramadan akwai wani dare mai falala mai suna kadar da aka saukar da Alkur’ani a cikinsa.

Wannan dare kuma shi ne mafi shaharar dare a cikin shekara, kuma lokacin gafarar zunubai, a cikinsa ne mala'iku suke sauka kasa, kuma a cikinsa za a kaddara shekara ta gaba ga bayi.

Tabbas Lailatul Kadr tana cikin watan Ramadan, amma ba a bayyana takamaiman lokacinta ba. An ambaci darare na 19, 21, 23 da 27 a matsayin yiwuwar faruwar Lailatul Kadri a cikinsu, inda aka fi mai da hankali kan daren 23 da 27 a dararen Ramadan. An nasiha ga masu imani a wadannan darare da su farka har zuwa safiya, su kuma gabatar da addu'o'i.

Nau'i biyu na saukar Alqur'ani

Kur'ani ya sauka sau biyu, sauka ta  a lokaci guda, da kuma kuma sauka a hankali matak-mataki. An saukar da Alkur'ani ga Annabi (SAW) a daren Lailatul kadari baki dayansa, ma’ana dukkanin abin da ke cikin kur’ani Allah ya sanar da manzon Allah shi a wannan daren, amma kuma a hankali-hankali ayoyi suka rika sauka cikin tsawon shekaru 23 har zuwa karshen rayuwarsa mai albarka, bayanin ayoyin yana nuni da haka kuma ruwayoyi da yawa sun tabbatar da haka.

Da yake bayyana saukar Alkur’ani, Allamah Tabatabai ya ce: “Alkur’ani fiye da yadda muka fahimta yake, amma dai har kullum abin da ke cikinsa shi ne gaskiya, wada ba za ta taba canjawa ba, ko mun fahimci hakan ko ba mu fahimta ba.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3720584

captcha