Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Shafaq cewa, sama da masu ziyara miliyan daya sun hallara a haramin Imam Ali (AS) a daren shahadar Imam Hammam har zuwa wayewar gari, sun karanta addu’ar Joshan Kabir tare da karatun kur’ani.
Ofishin yada labarai na Haramin Imam Ali (AS) da ke birnin Najaf Ashraf ya sanar da cewa, bisa kididdigar da aka samu, adadin maziyartan a daren na biyu a Najaf Ashraf ya haura miliyan uku.
A cewar majiyar, an gudanar da taron a daren jiya cikin kwanciyar hankali da tsauraran matakan tsaro, kuma ba a samu wata ta tsaro ba.