IQNA

Masu Fafutuka A Pakistan Sun Gargadi Gwamnatin Kasar Kan Yunkurin Kulla Alaka Da Isra’ila

19:06 - April 28, 2022
Lambar Labari: 3487227
Tehran (IQNA) Wasu gungun masu fafutuka ta addini da ta siyasa a Pakistan sun yi gargadi kan kokarin da gwamnatin Pakistan ke yi a boye na daidaita alaka da gwamnatin Isra’ila.

Shafin yada labarai na Down ya bayar da rahoton cewa, masu jawabai a jam'iyyun siyasa da na addini da dama a taron Quds a Islam-abad sun gargadi gwamnati kan kokarin daidaita alaka da gwamnatin Isra’ila, inda suka zargi sabuwar gwamnatin ta Pakistan da aiwatar da wani shiri kan hakan a asirce.

Gidauniyar Falasdinu ta Pakistan ce ta shirya taron a daidai lokacin da ake gudanar da taruka na ranar Quds, wanda kuma za a gudanar da babban gangami da jerin gwano a duk fadin kasar ta Pakistan a ranar Juma'a mai zuwa ta karshen watan Ramadan.

Baya ga ‘yan kasar Pakistan dalibai Falasdinawa da dama da suke karatu a jami'o'in kasar su ma sun halarci taron.

Sakatare Janar na gidauniyar Saber Abu Maryam ya ce, ya damu matuka da cewa Pakistan za ta iya kulla alaka da Isra'ila sakamakon wasu kasashen musulmi da suka kulla huldar diflomasiyya da ita.

Ya ce "Kada a manta cewa Mohammad Ali Jinnah, wanda ya kafa Pakistan, ya bayyana manufofin Pakistan game da Falasdinu a cikin 'yan watannin farko na samun 'yancin kan kasar Pakistan, kuma wannan manufar tana nan daram." in ji shi.

Ya kara da cewa duk da "yarjejeniyar karni" da gwamnatin Trump ke marawa baya da kuma "yarjejeniyar Abraham" da Biden ke goyon bayanta, kasashen musulmi hudu ne kawai suka mika wuya ga wannan manufa ta Amurka.

Liaqat Baluch, babban sakataren kungiyar Jamaat-e-Islami ya bayyana a wajen taron cewa: A lokacin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan Falasdinawa a cikin masallacin Al-Aqsa a cikin wannan watan Ramadan, babu wani mataki na a zo a gani da kasashen larabawa suka dauka kan hakan domin ladabtar da Isra’ila.

 

https://iqna.ir/fa/news/4052348

captcha