IQNA

Kungiyar OIC Ta Fitar Da Bayanin Goyon Bayan Falastinu Da Kare Masallacin Quds

20:38 - April 28, 2022
Lambar Labari: 3487229
Tehran (IQNA) Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta fitar da sanarwa inda ta jaddada cewa masallacin Aqsa yana matsayin jan layi ga musulmi.

Da yake jawabi a wajen taron kwamitin kula da harkokin Falastinu na kungiyar hadin kan kasashen musulmi, wanda aka shirya domin kare Kudus da Palastinu, wanda ya samu halartar daruruwan fitattun malaman addinin Islama da magoya bayan Palastinawa daga kasashe 40, Khaled Mashaal ya ce dabarun makiya yahudawan sahyoniya sun ginu ne a kan mamayar yankunan Palastinu, Kuma gwamnatin yahudawan ta kowace hanya tana kokarin kammala yakin a masallacin Aqsa.

Mashal ya bayyana cewa al'ummar Palastinu da suka dogara da hakkinsu a birnin Kudus da kuma masallacin Al-Aqsa, sun yi jarumtaka wajen nuna adawa da zaluncin haramtacciyar kasar Isra'ila, tare da tabbatar da cewa wannan masallaci na musulmi ne kawai, kuma yahudawa ba su da wani hakki a kansa.

Ya bayyana cewa, duk da rashin daidaiton da ke tsakanin Falastinawa da yahudawa, da zalunci da fin karfin da ake nuna wa Falastinawa, amma al'ummar Palastinu sun nasara wajen hana tabbatar manufar yahudawan, wato shafe Falastinu daga doron kasa.

Mashal ya ce: abin da ya faru a baya-bayan nan a masallacin Aqsa, wasu gungun matasa Palastinawa masu fafutuka a masallacin Aqsa, wadanda suka tashi tsaye a madadin al'umma baki daya, don kare alkiblar musulmi ta farko.

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a wajen Falastinu ya jaddada cewa, abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun tabbatar da cewa rayuwa ta hakika tana nufin rayuwa karkashin tutar sadaukarwa da tsayin daka domin kare karamar al’umma da kuma wurarenta masu tsarki.

 

4052507

 

 

captcha