IQNA

Tafsirin kur'ani na kasar Sin a dakin kur'ani na kasar Bahrain

17:17 - May 09, 2022
Lambar Labari: 3487269
Tehran (IQNA) An ajiye kwafin kur'ani mai tsarki da harshen Sinanci a dakin kur'ani na kasar Bahrain kuma an buga tare da rarraba dubunnan kwafi.

A rahoton iqna,  Wannan Kur'ani cikakke sassa 30 ne kuma ainihin rubutunsa ana ajiye shi a Taipei.

An buga da rarraba takaitattun adadi (kusan kwafi dubu) na wannan kur'ani a tsakanin musulmin kasar Sin a matsayin kyauta.

Wannan juzu'i na kur'ani yana da cikakken jerin ayoyi da batutuwa, kuma a karshensa akwai shafi kan fassarar wasu kalmomi na kur'ani a harshen Sinanci.

Wanda ake kira; Mai fassara alhazan Abdul Rahman Chan Ji Tavan ya mika wannan kwafin kur'ani ga Sheikh Khalid Tijoo, shugaban kungiyar musulinci ta kasar Sin a lokacin.

4055510

Abubuwan Da Ya Shafa: kalmomi ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha