IQNA

Taron Jana'izar 'yar Jarida Bafalasdiniya Abu Akleh da aka kashe

Tehran (IQNA) An gudanar da jana'izar 'yar jaridar Falasdinawa Shireen Abu Akleh da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kashe a ranar Juma'a a gabashin birnin Kudus.

Sojojin yahudawan sahyoniya sun kai hari kan masu gudanar da janaza a wajen taron, inda suka jikkata tare da kame mutane da dama.