IQNA

23:11 - May 20, 2022
Lambar Labari: 3487315
Tehran (IQNA) Dubun dubatar Falasdinawa ne suka gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa, duk kuwa da matakan da 'yan sandan Isra'ila suka dauka.

A yau ne birnin Quds ya samu halartar dubban Falasdinawa domin gudanar da sallar Juma'a a masallacin Al-Aqsa, alkiblar musulmi ta farko.

‘Yan mamaya na yahudawan sahyoniya sun hana masallata  Falasdinawa shiga cikin birnin ta hanyar kafa shingayen binciken ababen hawa da ke shiga birnin Kudus.

Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da dubban Falasdinawa suka shiga birnin Kudus da kuma yankunan da aka mamaye a shekara ta 1948 tun da sanyin safiyar yau domin isa  masallacin Al-Aqsa.

Kungiyoyin gwagwarmayar Palastinawa sun sha bayyana cewa al'ummar Palastinu za su tsaya tsayin daka wajen yakar 'yan mamaya da laifukan da suke aikatawa a dukkanin bangarori, sannan kuma dakarunsu za su ci gaba da kare birnin Kudus da masallacin Al-Aqsa.

Dubun dubatar Falasdinawa ne suka gudanar da addu'o'i a masallacin Al-Aqsa duk da takunkumin da 'yan mamaya suka sanya. Ofishin bayar da tallafin Musulunci a birnin Kudus ya yi kiyasin cewa kimanin mutane 30,000 ne suka gudanar da sallar Juma'a a alkibla ta farko ta musulmi.

Masallacin Al-Aqsa, a matsayin babbar alama ta Musulunci da Falasdinu na birnin Kudus, a ko da yaushe ya kasance abin da ake yi wa barna daga bangaren gwamnatin mamaya, A baya-bayan nan hare-haren da 'yan sahayoniya a kan wannan masallaci ya kara tsananta.

 

4058360

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shingayen bincike ، birnin Kudus ، da sanyin safiyar yau ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: