IQNA

15:50 - May 23, 2022
Lambar Labari: 3487328
Tehran (IQNA) 'Yar wasan kasar Kuwait ta janye daga karawa da ‘yar wasan Isra’ila da nufin bayyana goyon bayanta ga al'ummar Palastinu

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadi al-Balad cewa, Kholoud al-Mutairi ‘yar wasan katan Kuwait ta fice daga gasar ne bayan da aka zayyana sunanta a gasar cin kofin duniya da za a yi a Thailand domin fuskantar wakiliyar gwamnatin sahyoniyawan.

Babbar sakatariyar kwamitin wasannin nakasassu ta Kuwait Sharifa al-Ghanim, a cikin wata sanarwa da jaridar Al-Ra'iyya ta kasar Kuwait ta fitar ta ce: Domin gwamnatin Sahayoniya ta kwace mana kasar Falasdinu, dole ne mu nuna rashin amincewa da halscinta.

Masu fafutuka na Kuwaiti sun yaba da matakin al-Mutairi. Abdallah al-Musawi wani mai bincike kan lamarin Palastinu ya bayyana cewa: Kuwait na ci gaba da zama a kan matsayinta a hukumance na kin amincewa da halascin Isra’ila. wanda kuma abin alfahari ne, domin daidaita alaka da Isra’ila cin amanar Palastinu ne.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, wasu 'yan wasa daga bangarori daban-daban na kasar Kuwait, sun ki fuskantar abokan hamayya yahudawan sahyuniya domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu.

4059088

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: gwamnatin sahyoniyawa ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: