IQNA

18:16 - May 24, 2022
Lambar Labari: 3487336
Fararen hula 30 ne suka mutu a wani harin ta'addanci da kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta kai a arewacin Najeriya.

A rahon kamfanin dillancin labaran Sputnik Arab, an kai harin ne a jihar Borno da ke kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Chadi wanda 'yan ta'addar Daesh suka kai.

Duk da cewa an kai harin ne a karshen makon da ya gabata, har zuwa yau Talata ba a samu labarin harin ba, saboda yadda ‘yan ta’adda suka yi zagon kasa a hasuyoyin sadarwa.

Galibin wadanda aka kashe din dai ma'aikata ne a hare-haren kungiyar ISIL da ta kai a baya.

Tun da farko dai masana harkokin tsaro da dama sun yi gargadin karuwar ayyukan ISIL a Afirka. Idan babu wata rundunar da za ta yaki wannan kungiyar ta'addanci ta fuskoki daban-daban.

Wasu sun yi gargadin cewa 'yan ta'addan za su iya kafa gwamnati a Afirka kamar yadda muka gani a cikin Iraki da Siriya a baya.

 

4059483

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: jihar Borno ، iyakar Najeriya da kasar Chadi ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: