Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alkhaleej.ae ya bayar da rahoton cewa, shugaban majalisar kur'ani mai tsarki na Sharjah Shirzad Abdul Rahman Tahir ya ce: "Wannan sigar kur'ani da ba kasafai ake samunsa ba, na daya daga cikin tsoffin kur’nai da aka rubuta da salon rubutu na musamman.
Ya kara da cewa: "Wannan tsohon juzu'in kur'ani ana kiransa "Kazan Basma", wanda ya shahara a Jamhuriyar Tatarstan.
Shirzad Abdul Rahman Tahir ya ce: Wannan kur'ani sakamakon kokarin malaman Tatar ne a tsawon tarihi kuma an bambanta shi da kyakkyawan rubutun Kazani mai suna "Basma".
Shugaban majalisar kur'ani mai tsarki ta Sharjah ya ci gaba da cewa: A lokacin ne aka buga kwafi biyu na wannan kur'ani, na farko na manya ne, kuma an buga shi mujalladi biyu manya-manya, amma na biyu kuma an buga shi mujalladi 10 ƙaramin bugu domin yara ƙanana.
A karshe ya ce: "Wannan kwafin kur'ani mai tsarki da ba kasafai ake samunsa ba, wata cibiyar buga littattafai ta Asiya ce ta buga shi a wancan lokacin."