IQNA

Isra'ila Ta Kashe Falastinawa Uku Cikin Kasa Da Sa'oi Asharin Da Hudu

17:37 - June 02, 2022
Lambar Labari: 3487373
Tehran (IQNA) Sojojin Isra'ila sun harbe wani matashi Bafalasdine a wani samame da suka kai a birnin Bethlehem, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin yammacin gabar kogin Jordan.

Sojojin Isra'ila sun harbe Ayman Mheisen mai shekaru 21 a duniya a wani artabu da ya barke a sansanin 'yan gudun hijira na al-Dheisha da ke kudancin birnin Bethlehem a wannan Alhamis, Wanda kuma Shi ne Bafalasdine na uku da sojojin Isra'ila suka kashe a yammacin gabar kogin Jordan cikin sa'o'i 24.

An harbi matashin a jikinsa, an kuma kai shi zuwa asibiti amma ya rasu  sakamakon raunukan da ya samu, kamar yadda kafar yada labarai ta Arab48 ta ruwaito, rahoton ya kuma kara da cewa a yayin samamen wasu sun samu raunkuna yayin da kuma aka tsare wasu.

Ko a ranar Laraba sojojin Isra'ila sun harbe dan jaridar Falasdinu  Ghofran Warasnah da wani matashi Bilal Kabaha a wasu harbe-harbe na daban-daban a yammacin gabar kogin Jordan da suka mamaye.

An harbi Warasnah mai shekaru 31 a kirji a kofar sansanin ‘yan gudun hijira na Al Arroub da ke kusa da birnin Hebron.

4061599

 

captcha