A cewar Ekna; Kungiyar malaman musulmi ta duniya a cikin wata sanarwa da ta fitar, wacce kwafinta ta samu ga IQNA, ta jaddada kariyar Manzon Allah (SAW) tare da bayyana hakan a matsayin wani aiki na addini.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar Ahmad al-Risuni da babban sakataren kungiyar Ali Qaradaghi, kungiyar ta bukaci kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC da ta gudanar da taron koli domin daukar matakan da suka dace kan masu cin mutuncin Manzon Allah (S.A.W) .
Sanarwar ta ce: "Abin da jam'iyyar masu wariyar launin fata a Indiya ke yi ga Manzon Allah (S.A.W) da musulmi da kuma kawar da wayewar Musulunci babban laifi ne da ya zama dole a yi Allah wadai da shi a bainar jama'a."
Sanarwar ta ce kungiyar malaman musulmi ta duniya na bibiyar lamarin da matukar damuwa a kan abin da ke faruwa a yankin na Indiya; Daga irin zaluncin da ake yi wa 'yan uwa Rohingya a Myanmar, zuwa abin da jam'iyyar Hindu masu wariyar launin fata ke yi wa Musulman Kashmir da sauran jahohin Indiya da cin mutuncin Manzon Allah (SAW) da Ummu Al-Muminin Aisha .