IQNA

An Bude masallacin farko a Venice

16:32 - June 12, 2022
Lambar Labari: 3487410
Tehran (IQNA) An bude masallacin farko a birnin Venice na kasar Italiya a wani biki da ya samu halartar jami'ai daga kungiyoyin Musulunci da na Kirista na kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na iqna cewa, Venice, cibiyar tarihi ta UNESCO, a yanzu ta samu sabon wurin ibada ga dubban musulmin da ke zaune a birnin.

An bude masallacin farko a Venice a wani biki da ya samu halartar wakilan al'ummar musulmin kasar Italiya da jami'an wannan birni a ranar Juma'a 11 ga watan Yuni. Al'ummar musulmin dubban musulmi ne suka sayi ginin tare da samun kudin shiga daga zakka da aka karba a Venice da kuma tashar masana'antu ta Mastra da ke kusa.

Yassin LaFram shugaban kungiyar musulinci ta Bologna da kuma kungiyar hadin kan musulmi ta kasar Italiya ya ce: Muna alfahari da wannan wuri domin wata shaida ce ta hadin kanmu.

An Bude masallacin farko a Venice

Ya kara da cewa: Yanzu haka wannan masallaci a bude yake ga kowa da kowa, godiya ga kundin tsarin mulkin kasar Italiya wanda ya baiwa 'yan kasar damar zabar addininsu. Shugaban kungiyar hadin kan musulmi ta Italiya ya ci gaba da cewa: Dukkan musulmin da ke zaune a wannan kasa suna son samar da kasar da ake mutunta kowa da kuma taimakawa wajen tabbatar da moriyar jama'a.

Sadmir Aliyevsky, shugaban kungiyar Islama ta Venice ya ce "Wannan masallacin da aka bude a wani birni mai al'adu daban-daban, kuma jama'a daga ko'ina cikin duniya ke ziyartan su a kullum, zai kasance yana da ayyuka da dama da kowa zai yi maraba da shi."

https://iqna.ir/fa/news/4063603

Abubuwan Da Ya Shafa: sauka
captcha