IQNA

An fara gasar haddar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Libiya

17:29 - June 14, 2022
Lambar Labari: 3487419
Tehran (IQNA) An fara gasar haddar kur'ani mai tsarki ta kasar Libya karo na 10 a birnin Benghazi tare da halartar wakilai daga kasashe 40.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kasar Libya cewa, a ranar Lahadi 12 ga watan Yuni ne aka fara gudanar da gasar hardar kur’ani mai tsarki karo na 10 a kasar Libya inda kasashen larabawa da na musulmi 40 suka halarta.

An fara gasar ne a cibiyar bunkasa kere-kere da ke birnin Benghazi na kasar Libya, tare da wakilai daga kasashe 40 da kuma wani dan kasar Libya.

Ofishin kula da harkokin kur'ani da hadisai na ma'aiki (SAW) mai alaka da babban daraktan kula da  harkokin addinin muslunci na kasar Libya ne ke gudanar da bikin karramawar haddar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a kasar Libya.

Kasar Libiya na daya daga cikin kasashen da suka haddace kur'ani mai tsarki a kasashen Larabawa da Musulunci. Kila mutane kadan ne suka san cewa Libya na da masu haddar Alkur'ani miliyan daya. Yawan masu haddar kur’ani a kasar nan ya kai kashi biyar, kuma ana daukar masu haddar kur’ani a matsayin wadanda suka kammala jami’a kuma suna karbar alawus.

4064084

 

 

captcha