Tehran (IQNA) Shugaban hedkwatar cibiyar Arbaeen Husaini (AS) ya sanar da cewa, an mika wa dakarun kare juyin juya halin Musulunci alhakin gudanar da aikin ziyarar Arbaeen daga waje nda ya ce: Ana sa ran masu ziyara 400,000 daga Iran za su shiga kasar Iraki a wannan shekara.

A wata hira da ya yi da IQNA, Sidmjid Mirahmadi, shugaban babban ofishin Arbaeen Hosseini (AS) ya bayyana dangane da masu ziyara daga waje da suka shiga Iran za su bar kasar zuwa zuwa Iraki domin ziyarar Arbaeen, inda ya ce za su yi amfani da iyakokin Iran wajen shiga da fita .
Ya sanar da shirye-shiryen kan iyakar Rimdan (iyakar da ke tsakanin Iran da Pakistan) don shiga da kuma fita kan iyakar Shalamcheh don fitar da masu ziyara daga kasashen Pakistan da sauransu ta iyakokin Iran zuwa Iraki.
Ya kara da cewa, a kowace shekara ana samun masu shigowa Iran domin zuwa Iraki daga kasashen duniya daba-daban, da hakan ya hada da masu bi ta hanyar jiragen sama, da kuma masu bin hanyoyi na iyakar kasa.