IQNA

Hajjin 2022: Kwanakin Karshe na Tsayawa Alhazai a Madina

TEHRAN (IQNA) – Alhazan da suka fara zuwa Madina a yanzu suna shirin barin garin zuwa Makka domin gudanar da aikin Hajji.

Masallacin Annabi (SAW) da ke birnin Madina al-Munawrah, wurin haduwa ne da dimbin al'ummar da suka taho daga kasashen duniya daban-daban domin gudanar da ayyukan Hajji.

Kwanakin karshe na kasancewar mahajjata a masallacin Al-Nabi gabanin Ihrami suna da wani yanayi na daban.

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masallacin annabi ، madina ، makka ، ayyukan hajji ، ihrami