Jagoran kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdul-Malik Al-Houthi ya bayyana cewa: Rundunar kawance da take yakar al’ummar Yemen da taimakon maha’inta a halin yanzu ta fi mai da hankali kan neman kwace iko da lardin Al-Jawf da ke yammacin kasar saboda tarin arzikin man fetur da ke yankin.
Sayyid Houthi ya fayyace cewa: Lardin Al-Jawf ya dauki tsawon shekaru yana fuskantar bakar siyasar zalunci tun daga mahukuntan kasar da suka gabata, inda ya janyo al’ummar lardin take fama da matsanancin talauci, amma da an yi amfani da tarin arzikin lardin, da Al-Jawf tana daga cikin sahun farko masu arzikin karkashin kasa da za su farfado da tattalin arzikin kasar ta Yemen.