IQNA

Cin Zarafin wata musulma da ke sanye da lullubi a Jamus

16:00 - July 12, 2022
Lambar Labari: 3487536
Tehran (IQNA) A wani mataki na cin zarafi da aka yi wa musulmi, wani Bajamushe a birnin Berlin ya yaga wa wata mata Musulma lullubi tare da lakada mata duka.

A cewar al-Sharooq, a wani yanayi na cin zarafin musulmi a Jamus, an tursasa wata mata sanye da lullubi a Berlin domin ta cire lullubin da ke a kanta.

A cewar jaridar Spiegel, wani maharin mai shekaru 37 da haifuwa ya yaga gyale na wata Musulma mai shekaru 39, sannan ya raunata a kai da saman jikinta.

Da take bayyana cewa an kai harin ne a wani gidan cin abinci da ke gundumar Vicenza, jaridar ta kuma bayar da rahoton wani harin wariyar launin fata a gundumar Prenzlauer Berg da ke Berlin a safiyar Juma'a, inda wani mutum mai shekaru 52 ya ci mutuncin wasu mata musulmi  biyu.

Haka majiyar ta bayyana cewa an kama maharin kuma an kai shi asibiti saboda wani hali da ba a saba gani ba kafin a sake shi.

4070387

 

captcha