IQNA

Nasrullah Ya Yi Gargadi Kan Hana Lebanon Fitar Da Danyen Manta Da Kuma Iskar Gas

15:32 - July 14, 2022
Lambar Labari: 3487544
Tehran (IQNA) Sayyid Hasssan Nasrullah ya gargadi Isra’ila da kasar Amurka cewa idan aka hana Labanon cin gajiyar arzikin dake cikin teku to ba za ta bari Isra’ila ta sayar da iskar gas da manfetur ba,
A wani jawabi da yayi ta gidan talabijin a jiya laraba sakatare janar din kungiyar Hizbulla ta kasar Labanon Sayyid Hasssan Nasrullah ya gargadi Isra’ila da kasar Amurka cewa idan aka hana Labanon cin gajiyar arzikin dake cikin teku to ba za ta bari Isra’ila ta sayar da iskar gas da manfetur ba,
 
Har ila yau ya kara da cewa dakarun sojin na hizbullah na ci gaba da sa ido a dukkan wauraren da yahudwan sahayuniya suke a gabar tekun faladinu da ta mamaye, kuma dakarun gwagarmaya a shirye suke suka yi amfani da sararin samani da teku da tudu wajen kai hari kan makiya domin kare hakkokin Alummar labanon
 
Acikin jawabin na say a kara da cewa shata iyakar teku yana da muhimmanci sosai kuma it ace sahihiyar hanya ta ceto kasar labanon da alummarta ba wai yaki na kwakwalawa ba. Kana ya yi kira ga mahukumtan kasar da su yi amfani da karfin yan gwagwarmaya wajen kwato yancin alummar kasar, a tattaunawar da za su yi da masu shiga tsakani na Amurka , kuma kada su bari kasar birntaniya da Iara’ila su yaudaresu
 
Da yake ishara game da barazanar da ministan yaki na isra’ila yayi kuwa nasarullah ya shawarce shi daya tambaya sojojinsu da suka sha kashi a hannun dakarun hizbullah a yakin shekara ta 2006 , yana mai jaddada cewa Hizbulla a yanzu tafi karfi ta sosai ta fuskacin dakaru da kayan yaki fiye da kowanne lokaci a baya.
 
 

4070726

 

 

captcha