IQNA

Taron Tashtgozari a Tehran

TEHRAN(IQNA) Imam Hassan Mojtaba Hussainiya da masallacin Ardebilis da ke birnin Tehran sun gudanar da taron Tashtgozari domin nuna juyayin watan Muharram.
Tashtgozari dai na daya daga cikin tsofaffin al'adun da al'ummar Iran musamman wadanda suka fito daga yankunan arewa maso yammacin kasar suke yi kafin shigowar watan Muharram.
 
A wajen bikin dai masu zaman makoki na dauke da banukan ruwa da ke nuna alamar ruwan kogin Furat wanda aka hana Imam Husaini (AS) da iyalansa da sahabbansa.