IQNA

An Nada Tsohon Shugaban Nijar Muhamamdu Issoufou A Matsayin Mamba A Majalisar Fitattun Musulmi

16:18 - August 04, 2022
Lambar Labari: 3487637
Tehran (IQNA) Sheikh Al-Azhar Ahmad Tayyeb  ya nada tsohon shugaban kasar Nijar a matsayin daya daga cikin mambobin majalisar fitattun musulmi masu tasiri ta kasa da kasa.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran WAM ya bayar,  Sheikh Ahmad al-Tayeb, Sheikh na Al-Azhar ya zabi Muhammadu Issoufou tsohon shugaban kasar Nijar a matsayin mamba a wannan majalisa, saboda irin rawar da ya taka a lokacin mulkinsa, wajen ganin an samu sulhu da fahimtar juna tsakanin musulmi da sauran mabiya addinai.

Majalisar dai tana a matsayin mai zaman kanta wadda aka kafa a ranar 19 ga Yuli, 201, kuma Manufar kafa wannan majalisa ita ce karfafa zaman lafiya a tsakanin al'ummar musulmi, da kuma hada manyan malamai da masana da dattijai wadanda suka shahara da hikima da adalci da 'yancin kai da kuma kawo daidaito.

Sannan yana daga cikin manufofin majalisar, taimakawa wajen karfafa zaman lafiya a cikin al'ummomi hard a wadanda ba musulmi ba, da kuma rage yawan tashin hankali da yake-yake da suka faru a cikin wasu kasashe na musulmi a baya-bayan nan, da kuma kokarin magance sabanin da ke tsakanin kasashen musulmi.

Issoufou ya kasance shugaban kasar Nijar daga shekarar 2011 zuwa 2021, kuma kafin nan ya rike mukamin firaminista daga Afrilu 1993 zuwa Satumba 1994.

A watan Maris din shekarar 2021, tsohon shugaban kasar Nijar ya lashe lambar yabo ta "Mo Ibrahim", wadda ke daya daga cikin fitattun lambobin yabo a nahiyar Afirka, wadda ake ba wa shugabanni da suka yi nasara ta fuskar shugabanci.

 

4075736

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha