IQNA

Salah Ya Bayar Da Gudunmawa Domin Taimaka Ma Majami'ar Kiristoci da Gobara ta Shafa a Masar

9:22 - August 18, 2022
Lambar Labari: 3487708
Tehran (IQNA) Mohamed Salah ya ware makudan kudi domin sake gina wata majami’ar kiristoci da gobara ta kone ta kurmus a kasar Masar.

Tauraron kwallon kafa na duniya dan kasar Masar, Mohamed Salah da ke buga wasa a  kungiyar Liverpool a Ingila, ya ware kudi dala 156,000 domin sake gina wata majami’ar kiristoci  a kasarsa da gobara ta kone ta kurmus a cikin wannan mako, inda lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

A rahoton tashar Al-Arabiya, Mohamed Salah, tauraron kwallon kafa kuma kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Masar kuma tauraruwar kungiyar Liverpool ta Ingila, ya ware fam miliyan uku na kasar Masar kwatankwacin dalar Amurka 156,000 don taimakawa wajen sake gina Cocin Abu Sifin.

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi wata mummunar gobara a Cocin Abu Sifin da ke lardin Al-Giza na kasar Masar, inda mutane 41 suka mutu, wasu 14 kuma suka jikkata.

Jaridar Daily Mirror ta Ingila ta bayar da rahoton cewa,  Muhammad Salah ya shahara da irin wadannan ayyuka na jin kai a Ingila da kuma kasarsa ta Masar.

Jaridar Sunday Times ta Biritaniya a baya ta sanya Salah a matsayin mutum na takwas a tsakanin mutanen da suka  yawan kyauta a Biritaniya, da kuma bayar da tallafi na 2022.

Koa  cikin shekara ta 2019, Muhammad Salah ya bayar da kyautar makudan kudade ga cibiyar yaki da cutar daji a kasar masar, domin taimaka ma mutanen da suke fama da wannan cuta wadanda ba su da galihu, domin a yi musu magani.

 

4078867

 

 

captcha