IQNA

A karon farko;

Nadin mace a matsayin mai ba da shawara ga shugaban Azhar

15:37 - September 21, 2022
Lambar Labari: 3487889
Tehran (IQNA) A karon farko Sheikh Al-Azhar ya zabi mace a matsayin mai ba shi shawara.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sky News cewa, Sheikh Al-Azhar Ahmed Al-Tayeb ya zabi Dr. Nahle Al-Saeidi shugaban tsangayar ilimin addinin musulunci a birnin Alkahira a matsayin mai ba shi shawara.

Wannan dai shi ne karon farko da aka zabi mace a matsayin mai ba wa Sheikh Al-Azhar shawara, saboda shekaru da dama da suka gabata an kebe mukaman nasiha ga maza.

4086902

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karon farko ، nasiha ، maza ، sadarwa ، birnin Alkahira
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha