IQNA

Masu ziyarar Imam Ridha Suna Tafiya a kafa

MASHHAD (IQNA) – masu ziyara ne ke tattaki zuwa birnin Mashhad domin gudanar da tarukan zagayowar ranar shahadar limamin ahlul bait na takwas, Imam Ridha  (AS).

Dubban masu ziyara ne ke tattaki zuwa birnin Mashhad dake arewa maso gabashin kasar Iran, domin gudanar da tarukan zagayowar ranar shahadar limamin ahlul bait na takwas, Imam Reza (AS), a ranar 27 ga Satumba, 2022.