IQNA

Allah wadai da harin kunar bakin wake na Istanbul;

Al-Azhar ta kira hare-haren da ake kai wa fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba a matsayin harin ta’addanci

16:38 - November 14, 2022
Lambar Labari: 3488174
Cibiyar Musulunci ta Al-Azhar ta kasar Masar ta fitar da sanarwa inda ta yi Allah-wadai da harin ta'addancin da aka kai jiya a dandalin Taksim da ke birnin Istanbul na kasar Turkiyya .

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, cibiyar muslunci ta Azhar a kasar Turkiyya ta yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai a yammacin jiya 22 ga watan Nuwamba a birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Azhar a shafinsa na Facebook cewa: Azhar ta bayyana goyon bayanta ga jamhuriyar Turkiyya a cikin wannan mummunan lamari tare da jaddada cewa kai hari kan fararen hula almundahana ne a doron kasa kuma ya saba wa dukkanin al'amuran addini da na dan Adam.

Al-Azhar ta mika ta'aziyyarta ga al'ummar Turkiyya da kuma iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Kasashe da dama sun yi tir da harin ta'addancin da aka kai jiya a titin Esteghlal da ke tsakiyar birnin Istanbul na kasar Turkiyya, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 6 tare da jikkata wasu fiye da 80 na daban.

Ofishin jakadancin Moroko a Istanbul ya sanar a yammacin Lahadin da ta gabata cewa wasu mata 'yan yawon bude ido 'yan kasar Morocco biyu na daga cikin wadanda suka jikkata a wannan ta'addancin.

A sa'i daya kuma, jami'an sashen karamin ofishin jakadancin na ma'aikatar harkokin wajen kasar Turkiyya sun sanar da cewa babu wani dan kasar Iran da ya mutu a harin ta'addancin da aka kai a birnin Istanbul.

Ministan cikin gidan kasar Turkiyya ya kuma sanar da kame wata mata da ta kai harin bam a Istanbul inda ya kira kungiyar ta'adda ta PKK da ke da alhakin fashewar.

Nasser Kanani kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya kuma yi Allah wadai da wannan harin ta'addanci.

 

4099430

 

captcha