Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Arab News cewa, wannan rumfa mai duhu da ke cikin dakin baje kolin fasahar muslunci da ke birnin Jeddah na kasar Saudiyya ya samar wa maziyarta wuri mai matukar dacewa don kallon tsoffin ayyuka daga cibiyoyi masu daraja da kuma kasashen musulmi.
Wasu daga cikin mafi mahimmancin waɗannan ayyukan su ne ɗimbin kyawawan abubuwa da ayyuka na tarihi daga Uzbekistan, wasu daga cikinsu an baje su a karon farko. Wadannan ayyuka sun hada da Musxaf na tarihi da dama tare da taska na masaku da aka saka a wannan kasa ta tsakiyar Asiya, wadda a ko da yaushe tana da muhimmin matsayi a tarihin Musulunci.