IQNA

Farmakin Sojojin Isra'ila A Kan Musulmi Masu Sallar Asuba A Yau A Masallacin Al-aqsa

18:37 - March 27, 2023
Lambar Labari: 3488875
Tehran (IQNA) Dakarun mamaya sun kai farmaki ne da asuba a yau litinin, a harabar masallacin Al-Aqsa da masallacin Al-Qibli, inda suka kai auka kan masu ibada da karfin tsiya.

A rahoton kafofin yada labarai na cikin gida na Falastinu, dakarun da suka kai farmakin sun kwashe masu ibada daga harabar Al-Aqsa tare da kora su zuwa waje.

A halin da ake ciki dai sojojin mamaya sun mamaye gidajen mutanen da ke unguwar Bab Hatta da ke birnin Kudus, a daidai lokacin da rikicin ya barke tsakanin mazauna yankin da dakarun.

Haka nan kuma majiyoyin cikin gida sun ruwaito cewa sojojin sun yi barna a gidaje da dama.

Rahotanni sun ce ko a safiyar jiya Lahadi wasu gungun mahara sun kutsa kai cikin harabar Al-Aqsa, inda suka gudanar da al’adunsu na yahudawa a cikin masallacin mai alfarma.

 

 

4130105

 

captcha