IQNA

An bayar da gudummawar kwafin kur'ani mai tsarki 104,000 ga kasar Mauritaniya

13:49 - March 30, 2023
Lambar Labari: 3488890
Tehran (IQNA) Ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci, da'awah da jagorancin addinin muslunci ta kasar Saudiyya ta sanar da bayar da gudunmuwar  kur'ani mai tsarki 104,000 ga kasar Mauritaniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Khaleeyoun cewa cibiyar kula da kur’ani ta sarki Fahad ta kai kwafin kur’ani mai tsarki 104,000 ga jamhuriyar musulunci ta Muritaniya.

An buga wadannan kur’ani masu girma dabam dabam kuma an mika su ga mahukuntan wannan kasa a gaban jakadan Saudiyya a Mauritaniya.

Baitullah Ahmed Al-Asoud babban sakataren ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar Mauritaniya a jawabinsa game da wannan batu ya jaddada cewa wannan kyauta tana daya daga cikin mafi daraja da kimarta ta ruhi da ta zahiri fiye da kowace irin baiwa.

Ya kuma kara da daraja alakar da ke tsakanin masarautar Saudiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Mauritaniya tare da jaddada cewa babu wani abu da ya raba kasashen biyu, kuma tarihi, wayewa, da addini, da harshe, da alaka da zumunta da kuma makoma ta bai daya.

A baya dai an baiwa kasar Senegal kwafin kur'ani mai tsarki guda 120,000.

A cewar Abdul Latif Al-Sheikh, ministan kula da harkokin addinin muslunci na kasar Saudiyya, yawan kwafin kur’ani mai tsarki ya karu daga kwafi miliyan 9 zuwa kwafi miliyan 20 a duk shekara. A cewarsa, ya zuwa karshen shekarar 2021, sama da kwafin kur’ani mai tsarki miliyan 345 ne wannan majalisa ta buga.

Ya zuwa yanzu, fiye da kwafi miliyan 320 na tarjamar kur’ani mai tsarki a cikin harsuna sama da 76 ne aka rarraba a duniya ta hanyar buga wannan taro.

 

4130484

 

 

 

 

captcha