IQNA

Daga gobe yahudawa za su ci gaba da kai hare-hare a masallacin Al-Aqsa

20:05 - April 23, 2023
Lambar Labari: 3489026
Tehran (IQNA) Kungiyar yahudawan "Bidino" ta sanar da cewa daga gobe litinin za'a ci gaba da kai hare-haren 'yan sahayoniyawan yahudawan a masallacin Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cibiyar yada labaran Falasdinu cewa, wannan kungiya ta yahudawa mai tsattsauran ra’ayi ta kira mazauna yankin da su kai farmaki kan masallacin Al-Aqsa a yau Laraba a daidai lokacin da ake tunawa da kafuwar gwamnatin yahudawan sahyuniya.

Har ila yau, 'yan adawa masu tsattsauran ra'ayi na Isra'ila sun fitar da wani kira na kai hari kan masallacin Al-Aqsa a ranar Alhamis domin nuna goyon baya ga sauye-sauyen shari'a da gwamnatin Netanyahu ta shirya.

Hakan dai na faruwa ne duk da cewa al'ummar Palastinu sun yi kira da a ci gaba da gudanar da gagarumin biki a cikin masallacin Al-Aqsa ko da bayan watan Ramadan.

Wakilin Majalisar Dokokin Falasdinu daga birnin Quds Ahmed Attoun ya bukaci da a ci gaba da gudanar da gagarumin aiki a masallacin Al-Aqsa bayan watan mai alfarma da nufin kakkabe tsare-tsare da makirce-makircen makiya yahudawan sahyoniya kan wannan masallaci.

Attun ya yi nuni da cewa wajibi ne a gudanar da itikafi a cikin masallacin al-Aqsa a wasu watannin shekara ban da watan Ramadan, domin makiya yahudawan sahyoniya ba sa yin kasa a gwiwa wajen aiwatar da matakan da suke so a wannan masallaci.

Ya ce wani abin da ke gaban gwamnatin sahyoniyawa wajen aiwatar da tsare-tsaren yahudawa a cikin masallacin Al-Aqsa shi ne I'itikafi da kasancewar dindindin a masallacin Al-Aqsa.

 

 

4136079

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Masallacin Al-Aqsa yahudawa
captcha