IQNA

​Kasar Saudiyya ta karbi bakuncin mahajjata miliyan 99 a cikin shekaru 54 da suka gabata

17:43 - June 24, 2023
Lambar Labari: 3489363
Saudiyya ta sanar da karbar bakuncin mahajjata sama da miliyan 99 tun shekaru 54 da suka gabata har zuwa aikin hajjin bara.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, bayanai daga hukumar kididdiga ta kasar Saudiyya sun yi nuni da cewa sama da mahajjata miliyan 99 ne suka je Saudiyya a cikin shekaru 54 da suka gabata.

Wannan kididdigar dai tana da alaka ne da lokacin da hukumar kididdiga ta kasar Saudiyya ta fara gudanar da ayyukanta a shekara ta 1390 bayan hijira a karkashin sunan hukumar kididdiga ta kasa da kasa, kuma ta sanar da kididdigar har zuwa shekara ta 1443 bayan hijira, wato Hajjin bara.

Saudiyya ta yi hasashen sama da mahajjata miliyan biyu ne za su halarci aikin Hajjin bana, wanda za a fara a ranar Litinin 5 ga watan Yuli.

Sai in ce; Alhazai a shekarar da ta gabata sun kai dubu 899 353, daga cikinsu dubu 779 919 daga kasashen waje ne.​

 

4149919

 

captcha