A rahoton da kamfanin dillancin labaran Tass ya bayar, gungun wakilai da ‘yan majalisar dattijai ne suka gabatar da wannan kudiri a karkashin jagorancin Anatoly Aksakov, shugaban kwamitin kasuwannin hada-hadar kudi na Duma.
Za a gudanar da gwajin aiwatar da wannan kudiri a jamhuriyar Bashghuristan da Tatarstan da Chechniya da kuma Dagestan, kuma idan gwamnati da babban bankin kasar Rasha suka amince, mai yiyuwa ne wasu yankuna su shiga wannan kudiri.
Ana aiwatar da gwajin wannan kudiri na tsawon shekaru 2 daga ranar 1 ga Satumba, 2023 zuwa 1 ga Satumba, 2025, kuma gwamnati da babban bankin Rasha na iya tsawaita wannan lokacin.