IQNA

16:41 - July 21, 2023
Lambar Labari: 3489512

An fara karbar maniyyatan Umrah daga kasashen waje a kasar Saudiyya

Makkah (IQNA) Kasar Saudiyya ta fara karbar maniyyatan Umrah daga kasashen waje don shiga sabuwar shekara ta Hijira ta 1445.

An fara karbar maniyyatan Umrah daga kasashen waje a kasar Saudiyya

Shafin sadarwa na yanar gizo na “Middle East News” ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar aikin hajji da umra ta kasar Saudiyya ta jaddada yadda ake hada kai a cikin tsarin shirin na “Hidima Bakin Allah” domin samar da ingantattun hidimomi da baiwa mafi yawan musulmi damar gudanar da aikin Umrah.

 Ma'aikatar ta sanar da cewa: Wadanda suka zo daga wajen kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah da aikin Hajji a Masallacin Annabi (SAW) za su iya neman takardar biza ta lantarki ta dandalin "NASQ" domin saukaka hanyoyin shiga da masauki da sufuri.

 Ya kamata a ambaci cewa lokacin Hajji na 1444H ya kare ne a farkon watan Yuli.

 

 

4156737

 

umrah

captcha