IQNA

Kwamitin Sulhu Ya Yi Tir Da Harin Ta'addanci A Hubbaren Shah Cheragh A Shiraz Iran

15:03 - August 17, 2023
Lambar Labari: 3489657
New York (IQNA) Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta'addanci na baya-bayan nan a birnin Shiraz na Iran.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan harin ta'addanci na baya-bayan nan da aka kai kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da kuma masu ziyara a hubbaren Shah Cheragh da ke birnin Shiraz na kudancin kasar Iran.

A cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Larabar da ta gabata, mambobin majalisar sun ce ta'addanci a kowane irin salonsa, na  daga cikin manyan barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya.

Sun kuma jaddada cewa dole ne a hukunta masu aikata laifuka, da hada baki da su, da masu bayar da kudade da kuma masu daukar nauyin irin wadannan ayyukan ta’addanci, kuma a gurfanar da su a gaban kuliya.

Kwamitin ya kuma bukaci dukkanin kasashen duniya, bisa la'akari da wajibci na dokokin kasa da kasa da kuma kudurorin kwamitin sulhun da suka dace, da su hada kai da Iran da sauran hukumomin da abin ya shafa a wannan fanni.

 

 

4163099

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kudade mambobi majalisa ayyuka shiraz
captcha