Tashar Aljazeera ta samu hotuna da bidiyoyi da ke nuni da dimbin mayaka daga bataliyar Qassam sun kai hari a cibiyar soji ta Erez tare da kama wasu jami’ai da sojojin Isra’ila.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Aljazeera cewa, a lokacin yakin guguwar Aqsa, dakarun ‘yan adawa sun yi nasarar kutsawa cikin cibiyar soji ta Erez tare da kame wasu da dama daga cikin mahara yahudawan sahyoniya.
Har ila yau, mayakan na bataliyar al-Qassam sun kame kayayakin soji da dama da kuma motoci.