Gaza (IQNA) Dea Sharaf ‘yar jarida ‘yar Falasdinu ta yi shahada a yau (Alhamis) bayan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ke ci gaba da kaiwa a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Al-Alam cewa; Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun harba rokoki da dama kan gidan dan jaridar da ke yankin Al-Zawaida a tsakiyar zirin Gaza, lamarin da ya kai ga shahadar ‘yar jarida "Dua Sharaf" da danta, tare da shahadarta adadin ‘yan jarida da suka yi shahada a Gaza ya kai mutane 24.
A cewar rahoton, a daren jiya ne mayakan sojojin yahudawa ‘yan mamaya suka yi ruwan bama-bamai a yankunan Tel Al-Hawa, Al-Jawzat da titin Al-Nafq a cikin birnin Gaza, kuma an kai wani harin a kusa da filin wasa na Elimuk da ke tsakiyar birnin.