IQNA

Wata ‘Yar Jarida da karamin yaronta sun yi shahada a Gaza

14:22 - October 26, 2023
Lambar Labari: 3490042
Gaza (IQNA) Dea Sharaf ‘yar jarida ‘yar Falasdinu ta yi shahada a yau (Alhamis) bayan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ke ci gaba da kaiwa a zirin Gaza.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Al-Alam cewa; Jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra'ila sun harba rokoki da dama kan gidan dan jaridar da ke yankin Al-Zawaida a tsakiyar zirin Gaza, lamarin da ya kai ga shahadar ‘yar  jarida "Dua Sharaf" da danta, tare da shahadarta adadin ‘yan jarida da suka yi shahada a Gaza ya kai mutane 24.

A cewar rahoton, a daren jiya ne mayakan sojojin yahudawa ‘yan mamaya suka yi ruwan bama-bamai a yankunan Tel Al-Hawa, Al-Jawzat da titin Al-Nafq a cikin birnin Gaza, kuma an kai wani harin a kusa da filin wasa na Elimuk da ke tsakiyar birnin.

 

 

4177980

 

Abubuwan Da Ya Shafa: shahada birnin Gaza jarida mamaya yahudawa
captcha