IQNA

Canza lokacin babban taron shugabannin kasashen musulmi game da Gaza

18:24 - November 10, 2023
Lambar Labari: 3490124
Riyadh (IQNA) A yammacin ranar Asabar (11 ga Nuwamba) ne za a gudanar da taron kolin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi dangane da Gaza, wanda aka shirya gudanarwa a baya a ranar Lahadi (12 ga Nuwamba), a birnin Riyadh, babban birnin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin labaran Anatolia ya bayar da rahoton cewa, gobe da yamma ne za a gudanar da zaman babban taro karo na 8 na shugabannin kasashen kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Riyadh, da nufin gudanar da bincike kan harin dabbanci da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a zirin Gaza.

Shugabannin kasashen musulmi 57 mambobin kungiyar hadin kan kasashen musulmi za su hallara a wannan taro domin tattaunawa da musayar ra'ayi kan hare-haren wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai kan al'ummar Gaza da ake zalunta.

A cikin sanarwar da kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar, an bayyana cewa, za a gudanar da taron na musamman ne bisa gayyatar shugaban na lokaci-lokaci na wannan cibiya.

A cikin bayanin da ya gabata, yana mai nuni da cewa, za a tattauna irin munanan hare-haren da Isra'ila ke kai wa al'ummar Palastinu a cikin wannan taro, an bayyana cewa, an gudanar da taron share fage a matakin wakilan kasashe a ranar Alhamis 9 ga watan Nuwamba.

An kuma bayyana cewa, a gobe ne za a gabatar da shawarwarin da aka yanke a taron da aka gudanar gabanin taron a matakin ministocin harkokin wajen kasar domin amincewa da shi a babban taron koli na musamman na shugabannin kasashen musulmi karo na 8.

Za a gudanar da wannan taro ne da batun Palastinu, wanda shi ne babban batu na al'ummar musulmi, da kuma abubuwan da suke faruwa masu hatsarin gaske dangane da birnin Qudus, kuma manufar wannan taro ita ce kafa matsaya da daukar mataki na bai daya na Musulunci kan yaki da ta'addanci da ake ci gaba da yi  hare-haren da Isra'ila ke kaiwa al'ummar Palastinu.

 

 

 

4180967

 

captcha