Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya sanar da cewa, Falasdinawa 11,500 ne suka yi shahada sakamakon laifukan da sojojin yahudawan sahyoniya suka aikata a kan mazauna Gaza, kuma 4,710 daga cikin wadannan shahidan kananan yara ne.
Ita dai wannan hukuma ta gwamnatin kasar ta jaddada cewa sojojin gwamnatin sahyoniyawan mamaya sun aikata laifuka 1,200 a wannan yanki tun farkon harin da aka kai a Gaza.
Ofishin yada labarai na jihar Gaza ya bayyana cewa: An lalata gine-ginen gwamnati 95 sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza. Haka kuma, asibitoci 25 da cibiyoyin kiwon lafiya 52 ba su aiki a wannan lokacin.
Wannan hukumar ta gwamnati ta sanar da cewa: Mahara na Isra'ila sun aikata wani laifi na tarihi inda suka kai hari a asibitin Shafa a yau. Muna son bude mashigar Rafah nan take.
Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya jaddada cewa: "Saboda karancin man fetur, za a katse hanyoyin sadarwa a gobe, don haka muna gab da yin wani sabon laifi."
Kungiyar Hamas ta sanar da buga wata sanarwa cewa, ikirarin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta yi na gano makamai da harsasai a harabar asibitin Shefa ci gaba ne na karairayi da farfaganda mara tushe da nufin tabbatar da laifukan wannan gwamnati na lalata bangaren kiwon lafiya Zirin Gaza.
A yayin taron manema labarai na mako-mako da yake yi a hedkwatar kungiyar da ke birnin Geneva na kasar Switzerland, shugaban hukumar lafiya ta duniya Dros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana harin da sojojin mamaya na birnin Quds suka kai a asibitin Shafa da ke zirin Gaza da cewa abin da ba za a amince da shi ba ne.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya ya jaddada a kan haka: harin da sojojin Isra'ila suka kai a asibitin Shafa da ke Gaza abu ne da ba za a amince da shi ba, Asibitoci ba fagen fama ba ne.
Firaministan Spain Pedro Sánchez a wani jawabi da ya yi a yau ya sanar da cewa: Gwamnatin Spain za ta yi aiki domin amincewa da kasar Falasdinu.