Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Dustur cewa, Sheikh Mahmoud Shahat Anwar mai karatun addinin musulunci na kasar Masar ya jajanta wa al’ummar Palastinu ta hanyar yada wani faifan bidiyo a shafukansa na sada zumunta na Instagram da Facebook biyo bayan kazamin harin da sojojin yahudawan sahyuniya suka kai a zirin Gaza.
A bayan wannan faifan bidiyo mai kunshe da fage na laifuffukan baya-bayan nan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ta aikata a zirin Gaza, da ‘yan gudun hijira da kuma addu’o’i a masallacin Al-Aqsa, za a ji muryar wannan shahararren makaranci na Masar yana karanto aya ta 38 zuwa 40. na babin Hajji mai albarka.