Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al Mayadeen cewa, Sayyid Hassan Nasrallah, babban sakataren kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon, zai gabatar da jawabi a ranar Laraba mai zuwa 13 ga watan Disamba.
Majiyoyin labarai sun ruwaito cewa, za a gudanar da jawabin Sayyid Hassan Nasrallah da karfe 6 na yamma agogon kasar a ranar Laraba 13 ga watan Janairu, a daidai lokacin da ake cika shekaru hudu da shahadar kwamandojin gwagwarmaya, Sardar Soleimani da shahidan Abu Mahdi Al-Muhandis.
A cikin wannan jawabin ne ake sa ran Sayyid Nasrallah zai tattauna muhimman batutuwan da suka shafi yankin musamman yakin Gaza da kuma rikicin kan iyaka tsakanin kasar Labanon da gwamnatin sahyoniyawa.