IQNA

Bangaren kula da tsirrai da furanni na hubbaren Imam Hussain ya halarci baje kolin furanni na kasa da kasa a Bagadaza

16:33 - April 23, 2024
Lambar Labari: 3491033
IQNA - Sashen furanni da tsirrai na hubbaren Imam Hussaini  ya halarci bikin furanni da tsirrai na duniya karo na 13 da ake gudanarwa a Bagadaza.

Bangaren kula da tsirrai da furanni na hubbaren Imam Hussain ya halarci baje kolin furanni na kasa da kasa a Bagadaza

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Hubbaren cewa, sashen kula da furanni da shuka na  hubbaren Hosseini ya sanar da halartar bikin furanni da shuki na kasa da kasa karo na 13 a birnin Bagadaza. An gudanar da wannan baje kolin ne a wurin shakatawa na Al-Zora da ke birnin Bagadaza.

Jami'in sashen kula da furanni da shuka na hubbaren ya bayyana cewa: Bayan samun nasarar zama na daya a baje kolin shekaru  10 da suka gabata, sashen kula da furanni da shuka na hubbaren  ya halarci wannan biki shekara ta 11 a jere.

Wahab Alhar ya kara da cewa: Ingancin furanni da shuka na hubbaren a wannan biki ya sha bamban da shekarun baya.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, sashin fure da shuka na hubbaren Imam Hussain ya kasance a matsayi na farko.

4211854

 

 

 

 

 

captcha