IQNA

Mataimakin shugaban kungiyar kwararrun 'yan wasan dambe ta Amurka ya musulunta

21:27 - May 03, 2024
Lambar Labari: 3491087
Lauren Mack, mataimakin  shugaban kungiyar Professional Fighters League of America, babbar kungiyar ‘yan wasan dambe ya yi aikin  Umrah bayan ya musulunta a Makka.

Ali Walsh, jikan Muhammad Ali Kelli, ya yanke shawarar komawa Makkah  bayan nasarar da ya samu a gasar "Champions League of Professional Fighters" da aka gudanar a birnin Riyadh, domin kasancewa tare da Lauren Mack, mataimakin  shugaban was an dambe ta Amurka wanda ya musulunta .

Lauren Mack ya bayyana wannan shawarar a matsayin wani bangare na tunani na dogon lokaci dangane da dabi'u da ka'idojin Musulunci.

Yayin da yake bayyana farin cikinsa da tasirin wannan tafiya ta karfafa ruhi, Walsh ya ce: Wannan tafiya  ta kawo mani kwanciyar hankali mara misaltuwa, zan iya kwatanta shi a matsayin ainihin kusanci da Allah na hakika, wanda ya kara min karfi da azama a rayuwa.

Ya kara da cewa: Wannan tafiya za ta yi tasiri mai zurfi ba a fagen wasanni kadai ba, har ma da rayuwata ta ruhi.

Kungiyar kwararrun masu wasan dambe  ta yanke shawarar gudanar da wasannin gasar da za a yi a karon farko a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka. Za a bude wannan wasa  ne a ranar 10 ga Mayu a Riyadh.

 

4213566

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: musulunta tunani musulunci nasara ruhi
captcha