Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a safiyar yau Laraba, jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya gabatar da salla ga gawar Ayatullah Sayyid Ibrahim Raisi, shugaban Iran na 8 da kuma tawagarsa a jami'ar Tehran, tare da halartar miliyoyin al'ummar Tehran
Bayan kammala sallar, jagoran juyin juya halin Musulunci ya zo ga shahidai ya yi bankwana da wadannan shahidai ta hanyar karanta Fatiha.
Daga nan ne aka dauki gawawwakin shahidan hidima tare da rakiya zuwa dandalin Azadi tare da dimbin jama'a.