Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, a karshen makon da ya gabata ne sakatariyar kwamitin kula da aikewa da gayyato masu karatun kur’ani mai tsarki ta nada mambobin ayarin kur’ani na jamhuriyar musulunci ta Iran da aka aika zuwa aikin hajjin Tamattu a shekara ta 2024.