Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yaoum Sabi cewa, kasar Saudiyya ta sanar da ranar Juma’a a matsayin ranar farko ga watan Zul-Hijja.
Yayin da aka sanar da ganin jinjirin watan Zul-Hijja a hukumance, ranar 27 ga watan Yuni ne za a yi Idin Al-Adha a kasar Saudiyya.
A kalandar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ranar 28 ga watan Yuni ita ce Idin layya.